Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta gudanar da taron raya kafar intanet a karshen watan Nuwamba
2020-11-03 10:39:43        cri
Kasar Sin za ta gudanar da taro game da ci gaban kafar intanet, daga ranar 23 zuwa 24 ga watan Nuwamba, a Wuzhen dake lardin Zhejiang na gabashin kasar, inda za a gayyaci malamai da baki daga sassan gwamnatocin kasashen waje da hukumomin kasa da kasa da kuma kamfanoni.

A cewar mataimakin shugaban hukumar kula da kafar intanet ta kasar Sin, Zhao Zeliang, taken taron shi ne "karfafa fasahar zamani zai haifar da makoma mai haske- gina al'umma mai makoma ta bai daya a bangaren intanet".

Taron zai kunshi babban taro guda daya da wasu kananan taruka 5, da wasu shirye-shirye da za a yi ta intanet da kuma wandanda ba na intanet ba.

Babban taron zai mayar da hankali ne kan sabbin abubuwan yayi a fannin ci gaban intanet , ciki har da matakan kimiyya na yaki da annobar COVID-19. Kananan tarukan kuma za su tattauna kan ka'idojin kasa da kasa a fannin intanet da yadda masana'antu ke amfani da intanet da fasahar AI da sauransu.

A yayin taron, za a gabatar da rahotanni biyu kan ci gaban intanet, da suka hada da na kasar Sin da na duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China