Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi kira da kare 'yan Jarida
2020-11-03 10:28:26        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a kare 'yan jarida, a ranar da aka ware ta yaki da cin zarafin 'yan jarida ta duniya.

A sakonsa domin wannan rana, sakatare janar din ya ce idan aka kai wa 'yan jaria hari, illar na shafar dukkan al'umma. Kuma idan aka gaza kare su, to za a gamu da cikas wajen samun labarai da daukar sahihan matakai.

Ya kara da cewa, annobar COVID-19 ta kara barazana ga 'yan jarida da sauran ma'aikatan kafafen yada labarai, domin adadin abubuwan dake musu illa ya karu.

A cewarsa, an samu akalla hare-hare 21 kan 'yan jarida masu bayar da rahoto yayin da ake zanga-zanga a rabin farkon bana, adadin da ya yi daidai da baki dayan hare-haren da aka kai musu a cikin shekarar 2017. Baya ga haka, an samu karin abubuwan dake wa ayyukan 'yan jarida tarnaki, ciki har da barazanar gurfanar da su a gaban kuliya da tsarewa da daure su a gidan kaso da hana su gudanar da ayyukansu da kuma gazawa wajen aiwatar da bincike da hukunta wadanda suka ci zarafinsu.

Har ila yau, Antonio Guterres ya ce yayin da ake yaki da annobar COVID-19, yana jaddada kira da tabbatar da 'yancin aikin jarida da zai taka muhimmiyar rawa ga tabbatar da zaman lafiya da adalci da ci gaba mai dorewa da kuma kare hakkokin bil adama. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China