Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wane tasiri hadin gwiwar kafofin yada labaran Sin da Afrika zai yi a yaki da cutar COVID-19?
2020-11-02 16:05:59        cri

Wani babban al'amari da ya mamaye illahirin kafafen yada labaran kasa da kasa tun daga farkon wannan shekara ta 2020 shi ne batun barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19. Abu ne mai matukar wahala a wayi gari ba tare da an rawaito wani labari ko wasu rahotanni dake shafar annobar COVID-19 ba. Duba da yadda hankalin kafafen yada labaran duniya ya karkata kan batun yaki da wannan shu'umar cuta wacce ta gallabi dukkan kasashen duniya sakamakon halayyar rashin tabbas dake tattare da cutar inda a kullum take iya sauya halayyarta. Sai dai wani batu dake daukar hankula shi ne yadda ake yawan samun labarai da rahotanni masu cin karo da juna, har ma wasu kafafen yada labaran wasu sassan yammacin duniya ke neman siyasantar batun annobar ta COVID-19. Ko da yake, wannan bai zo da mamaki ba, domin mai halin baya fasa halinsa. Wannan dalili ne ma ya sa wakilai daga kafafen yada labaran kasar Sin da na kasashen Afrika a karshen makon da ya gabata suka bukaci a karfafa hadin gwiwa domin kalubalantar masu neman siyasantar da batutuwan dake shafar annobar ta COVID-19. Su dai wadannan wakilan sun bayyana hakan ne a wani taron kafafen yada labarai da suka gudanar ta intanet kan batun yaki da annobar. A cewar wakilan, ya kamata kafafen yada labaran su yayata hadin gwiwar da Sin da Afrika ke yi a kokarin kawar da annobar, kuma su bayar da gudummawa wajen farfadowar harkokin tattalin arziki, da kyautata rayuwar al'umma a kasashe masu tasowa bayan annobar. Taron ya cimma matsayar cewa, kafafen yada labarun za su rungumi tsarin cudanyar bangarori daban daban da kuma gudanar da harkokinsu bisa tsarin manufar MDD, kana za su ci gaba da goyon bayan hukumar lafiya ta duniya WHO a kokarin yaki da annobar COVID-19. Ko shakka babu, hadin gwiwar bangarorin biyu zai samar da kyakkyawan sakamako, da bayyana hakikanin halin da ake ciki, kana zai kawo karshen yadda wasu kafafen yada labaran yammacin duniya ke aron bakin kasashen na Sin da Afrika suna ci musu albasa babu gairi babu dalili. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China