Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan harajin da Sin ta rage ya zarce yuan triliyan 2 daga watan Junairu zuwa Satumba
2020-11-02 12:25:41        cri
Hukumar tattara haraji ta kasar Sin, ta ce yawan haraji da sauran kudaden da ake biya da kasar ta rage ya kai yuan triliyan 2.09, kwatankwacin dala biliyan 311, a cikin rubu'i 3 na farko a bana.

A cewar hukumar, daga cikin jimilar, an samu yuan triliyan 1.37 daga matakan rangwamen haraji da sauran kudaden da ake biya da Sin ta gabatar a bana, da nufin tallafawa ci gaban tattalin arziki da dakile annobar COVID-19.

Wani jami'in hukumar, Cai Zili, ya ce adadin masu biyan haraji na kasar ya karu da kaso 7.5 daga watan Junairu zuwa Satumba, inda a rubu'i na 3 aka samu karuwar kaso 26 cikin dari.

Ya ce sassan dake kula da tattara haraji, sun taimakawa Sinawa masu fitar da kayayyaki zuwa ketare, sauya akalar kasuwancinsu zuwa cikin gida ta hanyar fasahohin manyan bayanai, inda yawan cinikin da suka samu a cikin gida ya karu da kaso 7.7 cikin dari a cikin watanni 9 na farkon bana.

A cewarsa, kasar Sin za ta kara kokarin aiwatar da wasu matakan saukaka haraji da inganta hidimomin da ba sa bukatar biyan haraji ko kudi domin bunkasa harkokin kasuwanci. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China