Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana ra'ayinta game da nasarar Magufuli a matsayin shugaban Tanzania
2020-10-31 20:49:58        cri
Hukumar zaben kasar Tanzania ta sanar da sakamakon zaben kasar a jiya, inda shugaban kasar mai ci, John Magufuli ya lashe zaben da kaso 84.3 na kuri'un da aka kada.

Da aka nemi jin ra'ayin kasar Sin dangane da sakamakon zaben, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin, ya ce Sin na taya Magufuli murnar sake lashe zaben shugabancin kasar a wa'adi na biyu. Kuma ta yi ammana cewa, karkashin shugabancinsa, Tanzania za ta ci gaba da samun ci gaba da nasarori, kuma kasar Sin na sa ran karfafa hulda da sabuwar gwamnatin kasar domin inganta dangantakarsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China