![]() |
|
2020-10-31 20:48:46 cri |
Da aka nemi jin ra'ayin kasar Sin dangane da sakamakon zaben, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin, ya ce Sin na taya Magufuli murnar sake lashe zaben shugabancin kasar a wa'adi na biyu. Kuma ta yi ammana cewa, karkashin shugabancinsa, Tanzania za ta ci gaba da samun ci gaba da nasarori, kuma kasar Sin na sa ran karfafa hulda da sabuwar gwamnatin kasar domin inganta dangantakarsu. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China