Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga shugaban kasar Seychelles
2020-10-31 17:09:11        cri
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na Seychelles, Wavel Ramkalawan, bisa sake lashe zaben shugabancin kasar.

Cikin sakon, Xi Jinping ya ce abotar dake tsakanin Sin da Seychelles na da dadadden tarihi, kuma dangantakarsu na habaka ba tare da tangarda ba, yana mai cewa, sun samu sabbin nasarori ta fuskar musaya da hadin gwiwa a fannoni daban- daban.

Ya kara da cewa, yana ba da muhimmanci matuka ga raya dangantakar kasashen biyu, kuma yana son hada hannu da Shugaba Wavel Ramkalawan wajen habaka hadin gwiwar kasashen biyu ta fannoni daban daban domin amfanawa kasashen biyu da al'ummominsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China