Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: COVID-19 ta bunkasa kirkire-kirkire a fannin lafiya a Afrika
2020-10-31 16:55:47        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce matasan nahiyar Afrika sun bullo da kirkire-kirkiren da za su shawo kan kalubalen dake da alaka da kiwon lafiya yayin da ake fama da annobar COVID-19.

Daraktar WHO mai kula da nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti, ta ce yanzu nahiyar na cikin wani sabon babin kirkire-kirkire a fannin lafiya, wanda ya samo asali daga annobar.

Alkaluman WHO sun nuna cewa, sama da kirkire-kirkire 120 a fannin lafiya sun samo asali daga nahiyar Afrika, tun bayan bullar cutar a farkon bana.

Ta ce Afrika ce ta mamaye kaso 12.8 na sabbin fasahohi 1,000 da aka samar a duniya domin karfafa tunkarar COVID-19 a muhimman bangarori, kamar na sa ido da bibiyar wadanda suka yi mu'amala da masu cutar da kuma jinya.

Afrika ta kudu ita ce ke kan gaba a fannin yawan adadin kirkire-kirkire dake da alaka da COVID-19 a Afrika, inda ta dauki kaso 13 cikin jimilar adadin, sai Kenya dake bi mata baya da kaso 10, sai Nijeriya da ta dauki kaso 8 da Rwanda mai kaso 6.

A cewarta, ganin yadda ake samun habakar kirkire-kirkire a fannin kiwon lafiya a Afrika lokacin annobar, abu ne mai karfafa gwiwa, ta na mai cewa, ingantattun dabaru da kyakkyawan muhalli da wadatar kudi abubuwa ne masu muhimmanci da za su kai ga samun alfanu mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China