Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da rahoton kungiyar Amnesty International kan ayyukan 'yan sanda
2020-10-31 16:46:43        cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya, ta yi watsi da rahoton kungiyar agaji ta Amnesty International na baya-bayan nan, wanda ya zargi jami'an rundunar da take hakkokin bil adama yayin zanga-zangar adawa da zaluncin 'yan sandan da aka yi a wasu sassan kasar.

Wata sanarwa da ta shiga hannun Xinhua, ta ruwaito Babban Sufeto 'yan sandan kasar Mohammed Adamu na cewa, 'yan sandan sun yi aiki bisa kwarewa da kai zuciya nesa, wanda ya kai ga rutsawa da wasu jami'an rundunar.

Wani rahoton da Amnesty International ta fitar a ranar Laraba, ya zargi 'yan sandan da harbi kan masu zanga-zangar lumana, lamarin da rundunar ta bayyana a matsayin mara gaskiya da ka iya mummunan tasiri kan jama'a.

Babban sufeton ya ce jami'an rundunar sun yi amfani da halatattun matakan tabbatar da zanga-zangar sun gudana cikin lumana a galibin wurare, inda suka rika bin masu zanga-zangar tare da tabbatar da ba su kariya.

Ya kara da cewa, ko a lokacin da zanga-zangar ta rikide zuwa rikici a wasu sassan kasar, jami'an sun yi matukar kai zuciya nesa tare da kaucewa amfani da karfi wajen shawo kan yanayin.

Har ila yau, shugaban 'yan sandan ya ce masu zanga-zangar sun kashe jami'ansa 22 yayin da wasu da dama suka raunata, inda wasu daga cikinsu ke cikin mummunan yanayi.

Bugu da kari, ya ce an lalata ofishoshin 'yan sanda 205 tare da wasu kadarorin gwamnati da masu zaman kansu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China