Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon kakakin majalisar wakilan Nijeriya ya yabawa Sin kan yakinta da cutar COVID-19
2020-10-30 14:59:52        cri

Kwanan baya, tsohon kakakin majalisar wakilan Nijeriya Yakubu Dogara ya bayyana a birnin Abuja fadar mulkin Nijeriyar cewa, kasar Sin ta cimma nasara a fannin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kuma ta cancanci yabo, dangane da taimakon da ta baiwa kasa da kasa wajen habaka hadin gwiwa a fannin yaki da cutar.

Ya ce, Sin tana kan gaba a wannan fanni, musamman ma idan aka kwatanta ta da wasu kasashen da suka kasa mai da hankali kan hana yaduwar cutar, wadanda suka yi tsokacin cewa, cutar ba za ta zama wata matsala ba. Amma, abin bakin ciki shi ne, a wadancan kasashe, akwai mutane masu yawa da suka rasa rayukansu sakamakon wannan cuta.

Kakakin ya kara da cewa, Sin ta baiwa Najeriya babban taimako ta hanyar samar da na'urorin jinya. Ban da haka kuma, likitocin da kasar Sin ta tura Nijeriyar, sun baiwa kasar kwarin gwiwa wajen yaki da cutar COVID-19. Shi ya sa, ya kamata a yi hadin kai, domin fuskantar wannan matsala tare, da kuma yaki da cutar yadda ya kamata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China