Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
In Babu Lafiyar Al'umma, Babu Zaman Al'umma Mai Matsakaicin Karfi
2020-10-30 15:40:57        cri

Hausawa kan ce, lafiya uwar jiki. Lafiyar al'umma, wani tushe ne na raya zaman al'ummar kasa da wayewar kai, kana kuma yana shafar dukkan al'ummar kasa. Yayin da kasar Sin take kokarin raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi, tana kuma dora muhimmanci kan kyautata lafiyar al'ummarta.

A baya, wuyar ganin likita da kuma kashe kudi da yawa wajen samun magani, sun dade suna addabar mutane. Musamman ma kamuwa da ciwo kan dakatar da masu fama da talauci su fita daga kangin talauci. A shekarun baya, kwamitin tsakiya na JKS da ke karkashin shugaban Xi Jinping, ya ba da umurnin zurfafa gyare-gyaren da ake yi a tsarin kiwon lafiya, a kokarin kara kyautata ba da inshorar lafiya a duk fadin kasar.

Ya zuwa karshen shekarar 2019, jama'ar Sin da yawansu ya wuce kaso 87 cikin 100 ne suka je asibiti, ko wurin ba da magani cikin mintoci 15. Mutane biliyan 1.35 ne suka samu inshorar lafiya.

A farkon shekarar da muke ciki, an samu bullar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a duniya, ciki had da kasar Sin, wanda ya zuwa ranar 29 ga wata, ta harbi mutane 44,351,001 a duk duniya baki daya, yayin da wasu fiye da miliyan 1 da dubu 16 suka rasa rayukansu.

Shugaba Xi Jinping ya umurci a mayar da rayukan al'umma da lafiyarsu a gaba da komai, kuma a yi iyakacin kokarin ceton rayukan mutane, inda gwamnatin kasar Sin ta biya dukkan kudin jinya. Duk da haka, a wasu kasashe, shugabanni sun nuna taurin kai da girman kai, ba su saurari masu ilmin kimiyya ba, sun mayar da siyasa a gaba da komai. Don haka yayin da kasar Sin ta samu nasarar dakile yaduwar annobar a kasar, da samun farfadowar tattalin arziki, a wadannan kasashe kuwa mutuwar mutane tana ci gaba da karuwa.

A zamanin yau, ana kara samun sauye-sauye a mabambantan sassan zaman al'ummar kasar Sin a kwana a tashi. Kyautatuwar salon zaman rayuwa ya daga matsayin lafiyar al'ummar kasar Sin sosai. Ya zuwa karshen shekarar 2019 da ta gabata, matsakaicin tsawon rayukan mutanen kasar Sin da za a kai ga samu, ya kai shekaru 77.3 da haihuwa, wato ya karu da shekara 1 bisa na yau shekaru biyar da suka gabata.

Bunkasuwar kasar Sin ta kyautata lafiyar al'ummar Sin biliyan 1.4, sa'an nan al'ummar Sin biliyan 1.4 masu koshin lafiya, suna kokarin raya zaman al'ummar kasar Sin mai matsakaicin karfi. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China