Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin Najeriya ta musanta zargin harbin masu zanga-zangar kin jinin musgunawar da 'yan sandan ke yiwa al'umma a Lagos
2020-10-28 21:20:48        cri
Rundunar sojojin Najeriya, ta musanta zagin da ake mata cewa, sojojinta sun harbi masu gudanar da zanga-zangar lumana da suka hallara a wani wuri a Lagos a makon da ya gabata, inda suke bukatar a kawo karshen cin zarafin da 'yan sanda ke yiwa jama'a.

Harbin dai ya faru ne a rukunin shagunan zamanin nan na Lekki Toll Plaza dake Lagos, cibiyar kasuwancin kasar, a lokacin da gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita a ranar 20 ga watan Oktoba, inda masu zanga zangar suka taru, inda ake zargin sojoji masu sanye da kayan sarki da aikatawa.

Wata sanarwa wadda ita ce ta farko da aka fitar tun faruwar wannan lamari na makon da ya gabata, runduna ta 81 ta sojojin kasar ta bayyana cewa, ko da yake ta shiga aikin dawo da doka da oda a Lagos, biyo bayan ayyana dokar hana fita da gwamnati ta sanya, amma sojojinta ba su yi wani harbi ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China