![]() |
|
2020-10-28 16:45:52 cri |
Ita dai AED wata na'ura ce dake bayar da agajin gaggawa, wacce ke iya sarrafa kanta don taimakawa masu fama da lalurar ciwon zuciya domin taimaka musu wajen yin numfashi. An yi amanna amfani da AEDs yana taimakawa matuka wajen ceto rayukan marasa lafiya dake da nasaba da cutukan zuciya. Tana da saukin sarrafawa da zarar an koyar da yadda ake amfani da ita, idan an gamu da matsalar ciwon zuciyar cikin mintoci hudu AED da CPR suna taimakawa matuka wajen farfadowar numfashin a matsayin agajin gaggawa na farko kafin a kai mutum asibiti.
Jaridar ta rawaito cewa, ana aikin bayar da horon samar da agajin gaggawa a kamfanonin jiragen karkashin kasar. Sama da kashi 80 bisa 100 na ma'aikatan jiragen karkashin kasar ne za a baiwa horo domin ba su shaidar kwarewar ayyukan bada agajin gaggawa game da yadda za su yi amfani da na'urar AEDs yadda ya kamata.
A shekarun baya bayan nan, an samar da na'urorin AEDs masu yawa a wuraren taruwar jama'a, kamar manyan kantuna, da gidajen sinima, da filayen jiragen sama. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China