2020-10-28 11:47:32 cri |
Malam Aliyu Abubakar ya ce ya ga babban ci gaban da kasar Sin ta samu, kuma ya taba ziyartar wasu wurare masu ban sha'awa a Beijing, ciki har da babbar ganuwa wato Great Wall. Game da taron FOCAC kuma, Aliyu Abubakar ya ce, taro ne mai amfani kwarai da gaske, musamman wajen inganta hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Haka kuma ya bayyana wasu daga cikin kusoshin gwamnati a tawagar Najeriya da suka halarci taron a wancan karo.
A cikin shirin na wannan sati, malam Aliyu Abubakar ya yi karin haske kan hadin-gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Najeriya, da yadda jama'a za su ci gajiya daga irin wannan hadin-gwiwa.(Murtala Zhang)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China