Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'o'in kasar Sin sun kara yawan dalibai masu bukata ta musamman
2020-10-28 10:18:37        cri

Kungiyar masu bukata ta musamman ta kasar Sin CDPF ta ce, kwalejoji da jami'o'in kasar Sin sun kara yawan dalibai masu bukatar musamman da suka dauka daga shekarar 2017 zuwa ta 2019.

An dauki jimillar dalibai masu bukata ta musamman 12,362 a jami'o'in kasar Sin a shekarar 2019, wanda ya zarce 10,818 na shekarar 2017 da kuma 11,154 na shekarar 2018.

CDPF ta gudanar da aiki tare da sassa masu ruwa da tsaki a shekaru da dama domin ganin an samar da guraben ayyukan yi ga dalibai masu fama da lalurar nakasa da suka kammala karatu ta hanyar wani shirin musamman na neman aikin yi ta intanet da wanda ba ta intanet ba da kuma ta hanyar dandalin ayyukan hidima ta intanet don taimakawa masu lalurar samun guraben ayyukan yi ko kuma kafa wuraren sana'o'i. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China