Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a hukunta wadanda suka harbi masu zanga-zanga a Najeriya
2020-10-27 19:42:53        cri
Gwamnan jihar Lagos a tarayyar Najeriya, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa, ana nan ana gudanar da bincike don gano wadanda suka yi harbi a rukunin shagunan zamani na Lekki Toll Plaza dake Lagos, cibiyar kasuwancin kasar ranar Talatar da ta gabata.

Wata sanarwa da gwamnan ya fitar Talatar nan, ya lashi takwabin kafa hukumar da za ta gudanar da cikekken binciki kan abin da ya faru, tare da hukunta wadanda ke da hannu a wannan ta'asa.

Ya ce, jama'a sun yi ikirarin cewa, an kashe musu 'yan uwa da abokai. Don haka, an kafa hukumar ce, domin ta zakulo dukkan abubuwan da suka faru, a kuma sakawa kowa, ta yadda iyalai za su gano jami'an da suka aikata wannan danyen aiki.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China