Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Sayayya ta yanar gizo ta karade gundumomi marasa wadata
2020-10-27 14:10:34        cri

Shirin kasar Sin na shigar da hada hadar sayayyar hajoji ta yanar gizo zuwa sassan gundumomin karkarar kasar, ya karade yankuna mafiya fama da fatara har 832.

Wata kafar watsa labaran kasar ta hakaito rahoton shekarar nan ta 2020, wanda aka fitar yayin taron karawa juna sani na birnin Guiyang dake lardin Guizhou, game da aikin kasa na rage fatara ta amfani da yanar gizo, wanda ya nuna yadda sayayya ta yanar gizo a wadannan gundumomi ta karu, daga kudin Sin yuan biliyan 180 a shekarar 2014, zuwa yuan tiriliyan 1.7 a shekarar 2019.

Rahoton ya kara da cewa, a halin yanzu, yawan yankunan kasar Sin da aka sada da babban layin sadarwa na yanar gizo ya karu daga kasa da kaso 70% kafin aiwatar da shirin samar da hidimar hanyoyin sadarwar na duk kasa, zuwa kaso 98% a yanzu.

Kaza lika adadin makarantun firamare da na sakandare dake kasar masu amfana daga layukan yanar gizo, shi ma ya karu daga kaso 79.2% a karshen shekarar 2016, zuwa kaso 98.7% ya zuwa watan Agustan shekarar nan ta 2020.

Kawo yanzu dai, burin samar da isasshiyar hidimar hanyoyin sadarwar intanet a kasar Sin ya tabbata, inda ta karade asibitocin dake yankunan mafiya fama da talauci, yayin da karin mazauna irin wadannan yankuna ke samun damammaki na amfana daga hidimomin yaki da talauci ta kafar intanet. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China