Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan siyasar Amurka za su ji kunya ganin yadda suke bata sunan shawarar "ziri daya da hanya daya"
2020-10-26 21:49:24        cri

A jiya ne sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya fara ziyarar aiki a kasashen Indiya da Sri Lanka da Maldives gami da Indonesiya. Manazarta na ganin cewa, makasudin ziyarar tasa shi ne tunzura kasashen su nuna adawa da kasar Sin. Kuma hakikanin gaskiya, wannan ba abun mamaki ba ne, ganin yadda Mike Pompeo ke yunkurin bata sunan kasar Sin a wurare da dama, musamman karyar da ya sha kitsa wa cewa, wai shawarar "ziri daya da hanya daya" na kirkiro "tarkon bashi", a wani yunkuri na hana kasashe da dama su hada kai da kasar Sin.

Yayin ziyararsa a kasashen Turai da dama kwanan nan, Pompeo ya sha bayyana cewa, wai kasar Sin ta sa kasashen dake cikin shawarar "ziri daya da hanya daya" fadawa cikin "tarkon bashi", abun da ya jawo adawa daga kasashen da dama. Alal misali, a yayin da yake ganawa da Mike Pompeo a farkon watan da muke ciki, firaministan kasar Croatia Andrej PLENKOVIĆ ya jinjinawa kokarin da kasar Sin take yi na kafa irin wannan tsari na inganta hulda da shawarwari a tsakaninta da kasashen dake tsakiya gami da gabashin Turai. Har wa yau, a yayin da kafar CNN take zantawa da shugaban kasar Kenya wato Uhuru Kenyatta, ta sha rura wutar rikici dangane da batun bashin da kasar Sin ta samar, sai dai shugaba Kenyatta ya ce, "mun ari kudi daga kasar Sin, amma mun ari kudi ma daga ita Amurka".

Alkaluman kididdigar asusun bada lamuni na duniya IMF sun nuna cewa, ya zuwa karshen bara, akwai kaso 40 na kasashen Afirka wadanda suka tsunduma cikin matsalar bashi, amma yawancinsu sun ari kudaden ne daga bankuna gami da kamfanonin kasashen Turai da Amurka. A don haka, idan ana son dora laifi kan wadanda suka sa kasashen Afirka fadawa cikin tarkon bashin, Amurka ce da wasu kasashen yammacin duniya.

Menene ma'anar shawarar "ziri daya da hanya daya" ga kasashen duniya? Abubuwan da suka wakana a shekaru 7 da suka wuce, sun riga sun amsa wannan tambaya. Babu tantama yunkurin Pompeo na bata sunan kasar Sin zai bi ruwa.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China