Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babbar jami'ar ofishin MDD a Geneva ta yaba da kokarin Sin wajen habaka cudanyar bangarori daban daban
2020-10-26 10:52:49        cri

Yayin da ake murnar cika shekaru 75 da kafa MDD, babbar jami'ar ofishin majalissar dake Geneva Tatiana Valovaya, ta zanta da wakilinmu na CMG, inda ta bayyana cewa, alkaluman binciken da aka fitar sun nuna cewa, yawancin al'ummun kasashen duniya suna goyon bayan MDD, kuma kokarin da kasar Sin take domin habaka cudanyar dake tsakanin bangarori daban daban a fadin duniya, zai kawo babban tasiri ga ci gaban ra'ayin, saboda a halin yanzu, ya dace a yi hakuri da juna yayin da ake gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, ta yadda za a cimma maradun samun ci gaba mai dorewa.

Yayin zantawar ta da wakilinmu na CMG, babbar jami'ar ofishin MDD dake Geneva Tatiana Valovaya ta bayyana cewa, ra'ayin da al'ummun kasashen duniya ke nunawa game da amfanin MDD yana da matukar muhimmanci.

Tun daga ranar 1 ga watan Janairun bana, babban sakataren majalisar Antonio Guterres, ya fara gudanar da tattaunawa a fadin duniya domin tunawa da cika shekaru 75 da kafa MDD, tare kuma da tattaunawa kan batu game da yadda za a ciyar da duniyarmu gaba, lamarin da ya kasance tattaunawa mafi girma a tarihi.

Babban jigon tattaunawar ya kunshi tambayoyi guda biyu, wato wace irin makoma kake jira?, da kuma wace irin MDD kake bukata?

A cikin mutane sama da miliyan daya da aka ji ta bakin su a fadin duniya, kaso 87 bisa dari suna fatan za a kara habaka cudanyar dake tsakanin bangarori daban daban, haka kuma suna fatan za a gudanar da karin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, kana suna goyon bayan ayyukan da MDD ke gudanarwa. Madam Valovaya ta ce, "Yawancin al'ummun kasashen duniya sun gaya mana cewa, ana kara shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a duniyarmu, idan aka kwatanta da yanayin da ake ciki kafin shekaru 75 da suka gabata, sakamakon kafuwar MDD, lamarin da ya nuna cewa, suna goyon bayan aikinmu, kuma ya zama wajibi MDD ta fahimci burin al'ummun kasashen duniya, haka kuma ta yi kokari domin cimma burinsu."

A hannu guda jami'ar ta yaba da kokarin kasar Sin, saboda har kullum tana nacewa kan ra'ayin cudanyar bangarori daban daban, kuma tana kokarin kiyaye tsarin kasa da kasa dake karkashin jagorancin MDD, baya ga nacewa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa. Game da hakan ta bayyana cewa, "Goyon bayan da kasar Sin take nunawa ra'ayin cudanyar bangarori daban daban yana da matukar muhimmanci, kuma ya dace a kara mai da hankali kan hakuri da juna, yayin da ake habaka cudanyar bangarori daban daban. Daukacin kasashen duniya, manya ko karama, suna da ikon samun wakilci, da nuna ra'ayi iri guda. Ko shakka babu, goyon bayan da kasar Sin, wadda take samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri take nunawa ra'ayin cudanyar bangarori daban daban, zai yi babban tasiri ga ci gaban ra'ayin a nan gaba."

Kan matsalar yaduwar cutar COVID-19 a sassan duniya a yanzu, sau da yawa, MDD ta sha yin kira ga kasashen duniya, da su hada kai domin dakile annobar tare. A kwanan baya ma kasar Sin ta sanar da cewa, ta shiga shirin samar da allurar rigakafin COVID-19 a hukumance, matakin da ya samu yabo daga fannonin zaman takewar al'ummar duniya.

Valovaya ita ma ta bayyana cewa, MDD tana mai da hankali matuka kan goyon bayan da kasashen da suka shiga shirin suke nunawa wannan muhimmin hadin gwiwa, wanda ke tsakanin bangarori daban daban, tana mai cewa, "Ina maraba da bangarori daban daban a fadin duniya su shiga wannan shirin, dole ne mu goyi bayan aikin da ake gudanarwa tsakanin bangarori daban daban, kuma dole ne mu goyi bayan aikin hukumar kiwon lafiya da jin kai ta duniya, saboda yaduwar COVID-19 ba matsalar kiwon lafiya ba ce kawai, kalubale ne ma na tattalin arziki, da kuma zaman takewar al'umma. Muddin shirin ya samu goyon bayan kasashe mambobin MDD, hakan zai taka rawar gani a wadannan fannoni yadda ya kamata."

A farkon bana, MDD ta fitar da shirin "aikin shekaru goma", inda ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki mataki cikin hanzari, domin tabbatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030. Valovaya ta bayyana cewa, "Yanzu muna gudanar da aikin nan na shekaru goma, dole ne mu gudanar da aikin a fannoni daban daban, tare kuma da yin hakuri da juna, da haka za a samu halartar gwamnatocin kasashe, da kungiyoyin kasa da kasa, da kungiyoyi shiyya shiyya, da hukumomi masu zaman kansu, da kuma kungiyoyi da ba na gwamnati ba. Ajandar ci gaba mai dorewa tana shafar fannoni daban daban, kamar su zaman lafiya da kwanciyar hankali, da ci gaban tattalin arziki, da daidaiton jinsi, da hakkin dan Adam da sauransu, duk wadannan suna da muhimmanci matuka ga bil Adama."

A karshe dai Valovaya ta bayyana cewa, akwai muhimmanci kafa hulda tsakanin bangarori daban daban dake yin hakuri da juna, yayin da ake gudanar da harkokin kasa da kasa a nan gaba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China