


A cikin 'yan watannin baya, a kan samu matsalolin kwace kayayyakin fararen hula da na tarzoma a kasar Sudan ta kudu sakamakon tabarbarewar tattalin arzikin kasar, sabo da haka, a kwanakin baya, rundunar sojojin MDD wadda ke tabbatar da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu, ta kafa wata tawagar dudduba yadda kananan rundunonin sojojin kasashe daban-daban, ciki har da kasar Sin suke share fagen aikin yaki da matsalolin tarzoma domin tabbatar da ganin an tafiyar da aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar kamar yadda ya kamata. (Sanusi Chen)