Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cutar COVID-19 ta halaka likitoci 16 a Najeriya
2020-10-20 10:55:49        cri
Shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Kwara dake yammacin kasar Baba Issa, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu likitoci 16 ne suka gamu da ajalinsu, yayin da suke aikin yaki da annobar COVID-19 a Najeriya

Baba Issa ya shaidawa manema labarai cewa, an tabbatar da wadannan alkaluma ne, daga jihohi 36 na kasar tun lokacin da annobar ta barke watanni 8 da suka gabata.

Issa ya ce, daga wancan lokaci zuwa yanzu, likitoci 1,031 ne suka shiga hadarin kamuwa da kwayar cutar a Najeriya, kuma 321 daga cikinsu sun kamu da kwayar cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China