Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu zanga-zanga sun fasa wani gidan yari a kudancin Najeriya
2020-10-20 10:50:34        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa,fursunoni da dama ne suka arce daga wani gidan yari jiya Litinin, bayan da wani gungun masu zanga-zanga suka fasa wani gidan yari a Benin na jihar Edo dake yankin kudancin Najeriya.

Da yake Karin haske kan lamarin, wani jami'in gwamnatin jihar mai suna Osarodion Ogie ya ce, lamarin ya faru ne, bayan da masu zanga-zangar suka rusa katangar hedkwatar cibiyar gyara hali dake birnin na Benin. Masu boren dai na zanga-zanga ne a dandalin Kings Square dake Benin, don nuna adawa da yadda 'yan sanda ke gallazawa jama'a.

Bayan aukuwar lamarin ne kuma, gwamnatin jihar Edo, ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a fadin jihar. Ya ce, gwamnati ta dauki wannan mataki ne, domin kaucewa barnata dukiyoyin da kaiwa jama'a da cibiyoyi hare-hare daga bangaren masu boren, dake fakewa da sunan #EndSARS".

A kwanakin nan, an gudanar da boren na "EndSARS" a sassan manyan biranen Najeriya, inda masu boren suke neman yin adalci ga wadanda rundunar 'yan sanda yaki da fashi da aka kirkiro a kasar (SARS) ta kashe ko ta galaza musu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China