Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojoji sun kashe mayakan BH da dama a Nijeriya
2020-10-20 10:11:36        cri
Rundunar sojin Nijeriya, ta ce sojojinta sun kashe mayakan BH da dama yayin wasu ayyukan da suka gudanar a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar John Enenche, ya ce luguden wuta da aka yi kan maboyar mayakan BH a yankin Dikwa na jihar a ranar Lahadi, sun sauka inda aka auna su.

Ya ce luguden wutan wani bangare ne na ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankin, yana mai cewa, an gudanar da ayyukan ne biyo bayan ayyukan binciken da suka nuna cewa akwai adadi mai yawa na 'yan ta'adda da kayayyakinsu a yankin.

Ya ce jiragen yakin da aka tura domin gudanar da ayyukan ne suka kai hare-hare yankin, lamarin da ya kai ga kashe 'yan ta'adda da adama da kuma lalata kayayyakinsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China