Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An dawo da wasannin kwallon kwando a Rwanda bayan dakatarwa na watanni 7 saboda annobar COVID-19
2020-10-19 13:30:05        cri
A ranar Lahadi an dawo da gasar wasannin kwallon Kwando ta kasar Rwanda ta shekarar 2019-2020 a Kigali, babban birnin kasar, bayan dakatar da wasannin tun a ranar 15 ga watan Maris sakamakon barkewar annobar COVID-19 a kasar.

Gasar kwallon kwandon mafi girma ta kasar Rwanda an dawo da ita ne a ranar 18 ga watan nan na Oktoba kuma za a kammala a ranar 24 ga watan Oktoban, inda tawagogi 'yan wasa 12 zasu buga wasan a wuri guda a babban filin wasa na birnin Kigali, Desire Mugwiza, shugaban hukumar shirya wasan kwallon kwandon Rwanda FERWABA, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho.

Mugwiza ya ce, domin daukar matakan dakile bazuwar annobar COVID-19, za a buga wasannin ne ba tare da 'yan kallo ba.

Kungiyoyin wasanni biyu da suka yi fice daga kowane rukuni su ne zasu shiga zagayen kusa na karshe, kuma za a buga gasar karshe ne a ranar 24 ga watan Oktoba.

A cewar shugaban tawagar 'yan wasan, tawagar kwararru da jami'an shirya gasar, an riga an yi musu gwaje gwajen cutar COVID-19 kuma zasu cigaba da zama ne a otel din gundumar Bugesera, dake lardin gabashin kasar, kuma ba za a ba su izinin fita ba har sai an kammala gasar.

Jami'in yace, hukumar wasannin ta FERWABA, ta dauki kwararan matakan kandagarkin cutar yayin da aka dawo cigaba da gasar, ya kara da cewa, tilas ne kowane mutum ya kiyaye da bin matakan kandagarkin annobar ta COVID-19 domin gudanar da gasar cikin nasara.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China