Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Uganda ta kama matafiya dauke da shaidar gwajin COVID-19 na bogi
2020-10-19 10:31:05        cri
Hukumomin lafiya na kasar Uganda a ranar Lahadi sun tsare wasu matafiya 24 da aka same su da shaidun gwajin cutar COVID-19 na jabu a filin jirgin saman kasa da kasa na Entebbe, mai magana da yawun hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta kasar ce ya sanar da hakan.

Vianney Luggya, jami'in yada labaru na hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta kasar ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, an kama fasinjojin ne bayan sun gabatar da shaidar PCR na gwaje gwajen cutar na bogi, a lokacin da ake tantance su a filin jirgin saman domin yin tafiya zuwa wasu wurare daban daban.

Luggya yace, an gano sun lalata shaidarsu ta PCR. Kuma an riga an mika su hannun jami'an 'yan sanda masu kula da filin jirgin saman domin gudanar da binciken yadda suka mallaki shaidun na jabu, domin hukunta su daidai da laifin da suka aikata na saba doka.

Jami'in ya bukaci al'umma dasu guji duk wani yunkurin mallakar shaidar PCR ta bogi domin akwai cikakkun hanyoyin da ake iya tantance shaidar gwajin ta gaskiya da kuma ta jabu.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China