Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Guinea
2020-10-19 10:12:27        cri

A jiya ne, 'yan kasar Guinea suka kada kuri'ar zaben shugaban kasar da 'yan takara 12 suka fafata, ciki har da shugaban kasar mai ci Alpha Condé.

Alkaluman da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta fitar, sun nuna cewa, sama da masu kada kuri'a miliyan 5 da aka yiwa rijista ne, ake sa ran za su kada kuri'unsu a kimanin runfunan zabe 15,000 da aka tanada.

Galibin ra'ayoyin jama'a na nuna cewa, akwai yiwuwar a sake zaben Condé kan wannan mukami.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China