Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu zanga-zanga sun kaiwa tawagar gwamna hari a kudancin Najeriya
2020-10-18 20:30:38        cri
An kaiwa tawagar Gboyega Oyetola, gwamnan jahar Osun dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya hari, masu zanga-zanga sun kai harin ne a ranar Asabar a Osogbo, babban birnin jahar.

Cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yau Lahadi, Timothy Owoeye, kakakin majalisar dokokin jahar Osun, ya tabbatar cewa, masu zanga-zangar kawo karshen rundunar 'yan sanda ta EndSARS da suke ta yin kiraye-kirayen a yi sauye-sauye a tsarin 'yan sandan Najeriya ne suka kaddamar da harin kan tawagar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China