Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Armenia da Azerbaijan sun cimma sabuwar yarjejeniyar tsakaita wuta don samar da agajin jinkai
2020-10-18 15:51:08        cri
Kasashen Armenia da Azerbaijan sun cimma matsaya kan sabuwar yarjejeniyar tsakaita bude wuta domin samar da kayayyakin jinkan al'umma a yankin Nagorno-Karabakh, wacce ta fara aiki daga karfe 20:00 na daren Asabar agogon GMT, ministocin harkokin wajen kasashen biyu ne suka sanar da hakan da yammacin ranar Asabar.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar Armenia, an dauki wannan mataki ne bayan sanarwar da shugabannin kasashen Faransa, Rasha, da Amurka suka fitar a taron wakilan kasashen kungiyar OSCE Minsk Group, mai rajin wanzar da tsaro da hadin gwiwa a nahiyar Turai a ranar 1 ga watan Oktoban 2020, da kuma sanarwar taron hadin gwiwa na OSCE Minsk Group na ranar 5 ga watan Oktoba, wanda ya dace da sanarwar Moscow ta ranar 10 ga watan Oktoban 2020.

Azerbaijan ta tabbatar da cimma yarjejeniyar a makamanciyar sanarwar.

Wannan ne karo na biyu da dukkan bangarorin suka cimma matsaya a cikin 'yan makonni. Yarjejeniyar farko an cimma ne a ranar 10 ga watan Oktoba, bayan doguwar tattaunawar sulhu da aka gudanar a Moscow a ranar 9 ga watan Oktoba, inda kasashen biyu suka dinga zargin juna da warware yarjejeniyar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China