Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakin karatu na manoma
2020-10-16 15:47:56        cri

Kowace ranar Jumma'a ranar ce ta haduwa ta masu karatu da malam Chen Zhaoyu ya shirya a unguwarsu da ke birnin Rugao na lardin Jiangsu na kasar Sin. A shekarar 2009, an kafa dakin karatu na manoma a unguwar, sai dai a lokacin littattafai 2600 ne kawai ake da su, adadin da ya karu zuwa 4684 a yanzu. Yara da manoma dake unguwar duk suna zuwa dakin don karatu. Don a karfafa musu gwiwar karatu, an kuma kafa kungiyar masu karatu, kuma 'ya'yan kungiyar su kan hadu a kowace ranar Jumma'a, don su yi musayar ra'ayoyi dangane da littattafan da suka karanta. A farkon kafa kungiyar, mutane biyu ko uku ne kawai inda a yanzu suka karu zuwa sama da 20.

Malam Chen Zhaoyu bai taba zaton samun damar karatu bayan ayyukan gona ba. Amma yanzu, baya ga karanta littattafai, ya kan kuma gutsara labaran da ya karanta ga mazauna unguwar. Daga labarai na tarihi da na yaki da kwari, kusan babu abin da bai sani ba.

Akwai irin wannan dakunan karatu kimanin 60 a birnin Rugao. Yanzu haka malam Chen Zhaoyu na shirin karanta shahararrun littattafai hudu na kasar Sin, don ilmantar da jikansa da zai shiga makarantar firamare game da al'adun kasar Sin. Ya ce, burinsa shi ne ya rika gabatarwa 'ya'yan kungiyar labarai masu armashi a tsawon rayuwarsa. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China