Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 1.6 yayin da AU ta bukaci a kara himma don dakile annobar
2020-10-16 11:04:13        cri
Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afrika ya kai 1,603,982 ya zuwa jiya Alhamis, hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Africa CDC ta sanar da hakan.

Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiyar kungiyar tarayyar Afrika, ta bayyana cikin sanarwar da ta fitar cewa, yawan mutanen da cutar ta kashe a nahiyar ya kai 39,122 ya zuwa ranar Alhamis, a yayin da yawan mutanen da suka warke daga cutar a fadin nahiyar ya kai 1,325,204.

Afrika CDC ta kara da cewa, kasashen da annobar COVID-19 ta fi shafa a nahiyar Afrika sun hada da Afrika ta kudu, Morocco, Masar, Habasha da Najeriya.

Yankin kudancin Afrika ne shiyyar da cutar COVID-19 tafi kamari ta fuskar yawan mutanen da suka kamu da kuma wadanda cutar ta hallaka. Sai shiyyar arewacin Afrika a matsayin yanki na biyu da cutar COVID-19 tafi shafa a Afirka.

Alkaluman da hukumar dakile cutukan ta fitar sun nuna cewa, kasashen Afrika 6 ne ke da kashi 90 bisa 100 na yawan sabbin masu kamuwa da COVID-19 tun daga makon jiya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China