Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Layin dogon da Sin ta gina na ingiza ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afrika
2020-10-13 11:07:42        cri

 


A jiya Litinin aka cika shekaru 20 da kafa dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC, wanda ya bunkasa zuwa wani muhimmin dandalin tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika, tare kuma da haifar da dimbin alfanu, ciki har da bunkasa harkokin tattalin arziki a kasashen Afrika.

Misali shi ne, Layin dogon Benguela, wanda ya kasance muhimmin aiki a Angola, da hada tekun Indiya da na Atlantika, ya kuma ratsa kasashen Tanzania da Zambia da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. Wannan layin dogo ya zama hanyar samun kudin shiga ga iyalai da dama a yankunan da ya ratsa.

Layin dogon Benguela mai tsawon kilomita 1,344 ya ratsa garuruwa na cikin kasar Angola, daga yankin yammaci ya ratsa garin Lobito, sannan ya bi ta garuruwan gabashin kasar da suka hada da Benguela da Huambo da Kuito da Luena, ya kuma mika zuwa garin Luau dake kan iyakar Angola da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Wannan layin dogo, ya ba da kwarin gwiwar kasuwanci ga mazauna yankunan, inda aka kafa kasuwanni a kusan dukkanin tashoshinsa.

Jacob Fumanhi Sachiata, misali ne na alfanun hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika. A kowanne mako, Jacob Sachiata mazaunin garin Luau na Angola, ke zuwa garin Lobito dake gabar teku, inda yake sayo abincin ruwa mai tarin yawa, da nufin sayarwa a kasuwar garinsu na Luau.

An mika layin dogon Benguela da kamfanin gina layin dogo na kasar Sin wato CR20 ya gina a garin Lobito, a ranar 3 ga watan Oktoban 2019.

A cewar kamfanin CR20, layin dogon da aka fara ginawa a watan Junairun 2006, daya ne daga cikin muhimman ayyukan da aka yi a Angola tun bayan yakin basasa.

Yayin ginin da ya shafe shekaru 10, kamfanin na kasar Sin ya samar da guraben aikin yi sama da 25,000 ga 'yan asalin yankin, sannan ya horar da sauran wasu ma'aikata 5000, ciki har da direbobi da masu gyaran lantarki da ma'aikatan sashen sadarwa.

A cewar kamfanin, a lokacin aikin ginin, iftila'i da nakiyoyi da cututtuka, sun yi sanadin mutuwar ma'aikata Sinawa 20 da 'yan asalin yankin 2.

Duan Zhihua, daya daga cikin ma'aikatan da suka yi aikin shimfida layin dogon, ya ce nakiyoyin da aka dasa tun lokacin yakin basasa, sun haifar da gagarumar matsala ga ayyukan sadarwa da na sufuri yayin ginin.

A ranar 30 ga watan Yulin 2019, jirgin kasan kasa da kasa na yawon bude ido mai suna "Pride of Africa" ya isa birnin Dar es Salaam ta Tanzania daga Benguela, wanda ya kaddamar da jigilar fasinja na farko a jirgin kasan da ya hada tekuna 2.

Layin dogon Benguela na Angola, shi ne bangare na karshe na layin dogo mai tsawon kilomita 4,300, da ake gani a matsayin gadar da ta hada manyan tekuna biyu. Wanda kuma ya taimaka sosai wajen inganta tsarin layin dogo a Afrika da kuma hada yankuna ta hanyar saukaka cinikayya da bunkasa tattalin arziki da dangantakar al'adu a nahiyar.

Darakta Janar na cibiyar kula da sufurin jiragen kasa ta Angola, Ottoniel Manuel, ya bayyana layin dogon Benguela a matsayin wanda ya kawo manyan alfanu ga mazauna yankunan da ya ratsa, tare da alamta abotar dake tsakanin al'ummun Sin da Angola.

Wannan layin dogo, wanda ke dakon kaya ton sama da miliyan 16 a shekara, na taka rawa wajen raya tattalin arzikin Angola da ma daukacin nahiyar Afrika. A watan Maris na 2018, jirgin dakon kaya na farko ya dauki bakin karfe daga DCR zuwa gabaar ruwa a garin Lobito na Angola, lamarin da ya sake kaddamar da cinikayya ta jirgin kasa a Angola, da ya gamu da cikas tsawon shekaru 30, sannan ya rage tsadar jigilar kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen dake layin ya ratsa, kamar DRC da Zambia.

Yayin da ake cika shekaru 20 da kafa dandalin FOCAC, Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce cikin shekarun da aka kafa dandalin, kasar Sin ta gina layukan dogo da titunan da suka haura kilomita 6,000 da tashoshin ruwa kusan 20 da manyan tashoshin lantarki sama da 80, inda dukkansu suka bunkasa ayyukan masana'antu a nahiyar da inganta karfinta na samun ci gaba da kanta.

Shi ma a nasa bangare, daraktan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin a Nigeria, Charles Onanaiju, ya ce karkashin dandalin FOCAC da shawarar Ziri daya da hanya daya, akwai muhimmiyar dangantakar da ta kai ga rage gibin ababen more rayuwa da nahiyar ke fuskanta.

Yayin da yake jagorantar taron Sin da Afrika kan yaki da annobar COVID-19, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya karfafawa bangarorin biyu gwiwar karfafa hadin kansu karkashin shawarar Ziri daya da hanya daya da gaggauta aiwatar da batutuwan da aka cimma yayin taron FOCAC na Beijing.

Peter Kagwanja, shugaban nazarin manufofin Afrika ta kasar Kenya, ya ce kaddamar da FOCAC a shekarar 2000, ya daukaka dangantakar bangarorin biyu zuwa wani sabon mataki, inda ya bude wani sabon babi ga tsarin hadin giwa a fannin raya masana'antu da ababen more rayuwa.

Shi kuwa ministan lafiya na kasar Namibia, kalumbi Shalunga cewa ya yi, dandalin ya taka rawar gani wajen karfafa dangantaka da abota da goyon baya tsakanin Sin da Afrika, kuma mutane da dama daga kasashen sun amfana matuka. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China