Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya ziyarci lardin Guangdong dake kudancin Sin
2020-10-13 10:05:24        cri

Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar, Xi Jinping, a ranar Litinin ya isa lardin Guangdong dake kudancin kasar domin fara rangadin aiki a lardin.

A birnin Chaozhou, Xi ya ziyarci wasu kayayyakin tarihin gargajiyar yankin, da suka hada da wata gada mai dadadden tarihi, da ginin wata kofar gari mai cike da tarihi da kuma zanen layukan wasu tituna masu dadadden tarihi, domin duba yadda ake kiyaye kayayyakin tarihi na gargajiyar wadanda aka gaje su daga kaka da kakanni, wadannan kayayyakin sun kasance wasu albarkatu ne da aka gaje su suna da matukar alfanu ga tarihi da ci gaban al'adun gargajiya da kuma yawon bude ido.

Daga bisani shugaban ya ziyarci kamfanin Three-Circle na Chaozhou, wani kamfanin samar da kayan latironi ne da kayayyakin sadarwa, inda ya duba yadda kamfanin yake kiyaye fasahohin cikin gida, da yadda yake tafiyar da ayyukansa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China