Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Niger ya gana da shugaban kasar
2020-10-10 15:31:53        cri

Jakadan Sin dake Niger Zhang Lijun ya gana da shugaban kasar Mahamadou Issoufou a kwanakin baya, inda Zhang Lijun ya godewa kasar bisa goyon bayan kasar Sin da take yi kan batun kare hakkin Bil Adama, tare kuma da jajanta mata game da bala'in ambaliyar ruwa da take fuskanta.

A nasa bangare, shugaba Mahamadou Issoufou ya yabawa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, inda ya ce, hadin kan kasashen ya taimakawa bunkasar tattalin arziki da al'ummar kasarsa, yana mai cewa, Niger na matukar godiya da wannan. Ya kara da cewa, Niger da Sin abokai ne dake goyon bayan juna, kuma ya yi imanin cewa, kasashen biyu za su taka rawa wajen kiyaye tsarin gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban da kafa zaman oda da dokar kasa da kasa mafi adalci da daidaito. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China