Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan uwa mata dake dogaro ne da aikin saka kayayyaki
2020-10-22 11:15:49        cri

 

 

 

 

 

'Yan uwa mata Yang Chaozhen da Yang Chaoli suna zaune ne a kauyen Tongzi na gundumar Pingbian mai cin gashin kanta ta kabilar Miao. Da ma sun kasance talakawa ne da aka yi rajista. Amma yanzu suna dogaro ne da aikin saka kayayyaki, zaman rayuwarsu na kara samun kyautatuwa. A cikin 'yan shekarun nan, gundumar Pingbian ta sa himma wajen bunkasa sana'ar saka sosai, ta yi kokarin ba da horo ga masu sana'ar dinki. A yanzu haka, an riga an kafa masana'antun saka guda 4 don kawar da talauci, da tashoshin aikin saka 8 da kuma cibiyoyin saka guda 20 da aka kafa a gidaje, domin wadanda suka jagoranci masu aikin saka su samu kudin shiga.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China