Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu sa kai suke tsabtace shara da aka tara a rairayin bakin teku
2020-10-19 15:10:11        cri

 

 

 

 

Wannan ne yadda masu sa kai suke tsabtace shara da aka tara a rairayin bakin teku a Jarroy Marina a Dakar, babban birnin Senegal. Akwai mazauna kusan 40,000 a Jarroy Marina, yawancinsu suna rayuwa ne ta hanyar dogaro kan sana'ar kamun kifi. A lokacin damina daga watan Agusta zuwa Oktoba na kowace shekara, ruwan sama mai ƙarfi da ruwan teku suna kwaso datti mai yawa zuwa ruwan teku, hakan ya kawo barazana ga lafiyar masu yawon bude ido da mazauna yankin. Masu aikin sa kai suna fatan ta irin wannan aikin tsaftar, za a dawo da kyakkyawan yanayin bakin teku, ta yadda za a kara jan hankalin masu yawon bude ido na cikin gida da na waje, da kuma taimakawa masunta wadanda ke fama da talauci sakamakon raguwar albarkatun kamun kifi don kara kudin shigarsu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China