Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jihar Lagos a Najeriya ta sha alwashin aiwatar da tsauraran matakai kan gidajen mai
2020-10-09 21:07:22        cri
Gwamnatin jihar Lagos dake kudancin Najeriya, ta sha alwashin aiwatar da tsauraran matakai da ka'idoji, kan gidajen mai dake cinikayyar iskar gas, da ma sauran sinadarai masu saurin kama wuta, biyowa bayan wata fashewa a wani gidan mai da ta haifar da mummunar gobara a jihar.

A kalla mutane 8 ne aka tabbatar sun rasu, yayin gobarar iskar gas din da ta auku a jiya Alhamis, a wani gidan mai dake unguwar Baruwa, wadda ke wajen birnin na Lagos cibiyar kasuwancin kasar.

A yau Juma'a, gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu, ya fitar da wata sanarwa, dake nuna matukar kaduwarsa bisa aukuwar gobara, wadda ta hallaka mutane da barnata dukiyoyi, al'amarin da ya ce ya yi matukar bakantawa gwamnatin sa rai.

Gwamnan ya ce rahotannin farko da aka samar, sun nuna cewa, akwai sakacin aiki a bangaren mahukuntan gidan man, wanda hakan ya sabbaba tashin gobarar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China