Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin yawon bude ido na kasashen G20 zasu fadada gudunmawar fannin ga cigaban tattalin arziki
2020-10-08 17:00:23        cri

A jiya Laraba ministocin yawon bude ido na kasashen G20 sun cimma matsayar fadada gudunmawar da fannin yawon bude idon zai bayar wajen samar da dawwamamman cigaba.

Ministocin sun bukaci a kara bunkasa fannin yawon bude ido a matsayin wani muhimmin ginshiki kuma fanni mai karfi, ta yadda zai bayar da babbar gudunmawa ga cigaban tattalin arzikin duniya da samar da ayyuka masu tsoka, kamar yadda sanarwar ta G20 wanda kasar Saudiyya ke jagoranta ta fitar bayan kammala taronta.

Jami'an sun bayyana wasu manyan kalubaloli da annobar COVID-19 ta haifar da su, tare da gabatar da matakan da zasu taimaka wajen farfadowa da harkokin yawon shakatawa.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China