Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda birnin Xiamen ya bunkasa bayan da ya zama yankin musamman na tattalin arziki a kasar Sin
2020-10-08 16:54:11        cri


Ranar 7 ga wata, birnin Xiamen dake kusa da teku a kudu maso gabashin kasar Sin, ya cika shekaru 40 da zama yankin musamman na tattalin arziki. To ko ta yaya aka yi kokarin raya birnin har ya zama wurin dake jawo hankalin masu yawon bude ido, gami da jarin kasashen waje?

A shekara ta 1985, wani jami'in gwamnatin kasar Sin mai shekaru 32 ya fara aiki a matsayin mataimakin magajin garin birnin Xiamen, wanda ya soma kokarinsa na kara bude kofar birnin ga kasashen waje, domin kawo sauye-sauye da neman ci gaba. Sunan mutumin Xi Jinping.

Harkar sufurin jiragen sama, wata shaida ce ga yadda wani birni ke bude kofa ga sassan waje. A shekaru 30 da wani abu da suka wuce, filin jiragen sama dake Xiamen dan karami ne, kuma babu jirage da yawa. Xi Jinping wanda yake kula da harkokin kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Xiamen wato XiamenAir a wancan lokaci, ya yi bakin kokarinsa, har ya samu rance da yawansa ya kai dala miliyan 18 domin fadada filin jiragen saman dake Xiamen, kana, kamfanin XiamenAir ya yi hayar wasu jirage kirar Boeing-737 domin sufurin fasinjoji. A halin yanzu, kamfanin XiamenAir yana mallakar jirage sama da 200, ya kuma kaddamar da hanyoyin zirga-zirga sama da 350.

A watan Afrilun shekara ta 2015, lardin Fujian, wato inda birnin Xiamen yake, ya zama yankin gwaji na gudanar da cinikayya cikin 'yanci kashin farko a kasar Sin. Hakan ya ba Xiamen damar karfafa hadin-gwiwar tattalin arziki da kasuwanci, da mu'amalar al'adu tare da kasashen dake halartar shawarar "ziri daya da hanya daya", har ma cinikin shige da ficen sa yana ta kara bunkasa, kuma layin dogon da ya hada Sin da Turai ya zama sabuwar hanyar da ake bi, wajen jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa.

A halin yanzu, wasu muhimman sana'o'i suna bunkasa yadda ya kamata a yankin cinikayya maras shinge na Xiamen, ciki har da cinikin waje, da sufurin jiragen sama, da hada-hadar kudi, da yawon bude ido da kere-keren sabbin abubuwa da sauransu.

Hakika, yadda birnin Xiamen ya samu bunkasuwa a wadannan shekaru, ya shaida irin kokarin da kasar Sin ta yi na aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. Zuwa watan Satumbar shekara ta 2020, kasar Sin ta kafa wasu yankunan gudanar da kasuwanci cikin 'yanci 21, har ma tana fadada bude kofarta ga kasashen waje. Ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasarsa za ta ci gaba da bude kofarta ga ketare, kuma za ta ci gaba da kokarin kawo sauki, da 'yanci ga harkokin kasuwanci da zuba jari, domin neman cimma moriya tare da sauran kasashe. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China