Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun ceto 'yan kasashen waje 5 a kudancin kasar
2020-10-08 16:30:33        cri
Wasu baki 'yan kasashen waje 5 da 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu sun kubuta bayan da sojojin Najeriya suka ceto su a yankin Niger Delta mai arzikin mai, hukumar sojojin kasar ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Mutanen sun hada da 'yan kasar Rasha uku, da dan kasar Ukraine, sai guda dan kasar Equatorial Guinea, sojojin sun yi nasarar kubutar da mutanen ne yayin samamen da suka kaddamar a maboyar 'yan bindigar, John Enenche, kakakin rundunar tsaron Najeriyar ne ya bayyana cikin wata sanarwa.

Enenche ya ce, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da ma'aikatan 'yan kasashen waje tun a ranar 9 ga watan Mayun shekarar 2020.

Bakin da aka kubutar suna samun kulawar likitoci a wani asibitin sojoji, kamar yadda Enenche ya bayyana.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China