Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nazari: Sinawa ne suka fi gamsuwa da yadda gwamnatinsu ta tunkari annobar COVID-19
2020-10-07 16:59:25        cri
Wani nazarin da aka gudanar, ya nuna cewa, al'ummar Sinawa ne suka fi gamsuwa da yadda gwamnatin kasarsu ta tunkari cutar COVID-19.

Kafar Daily Mail ta kasar Burtaniya dake bada rahoto a shafin intanet, ta ce malamai daga Amurka da Spaniya sun nazarci mutane kusan 13,500 daga kasashe 19 da annobar COVID-19 ta yi wa mummunan kamu, domin auna yadda suka dauki matakan da gwamnatocinsu suka dauka wajen tunkarar annobar.

An nemi mutanen su bada maki kan yadda gwamnatocinsu suka dauki batun annobar, ciki har da yadda matakan kulle suka yi aiki da karfin yin gwaji da kuma yadda aka kare mutane masu rauni a lokacin da aka samu bullar cutar da farko.

Sakamakon ya nuna cewa, Sinawa ne suka fi gamsuwa da yadda gwamnatinsu ta tunkari annobar, inda kasar Sin ta samu maki 80.5 bisa 100.

Daga cikin kasashe 5 dake kan gaba wajen samun maki akwai Korea ta kudu da ta samu maki 74.5 sai Afrika ta kudu mai maki 64.6, akwai India da maki 63.8, sai Jamus mai maki 61.32 da dai sauransu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China