Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda kasar Sin ke samun ci gaba babu tsayawa
2020-10-06 17:12:31        cri


Ranar 1 ga watan Oktobar shekara ta 2014, rana ce ta cika shekaru 65 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. A wajen liyafar murnar ranar da aka yi, shugaban kasar Xi Jinping, ya gabatar da wani muhimmin jawabi, wanda ya kasance karo na farko da shugaban kasar Sin ya yi jawabi a wajen irin wannan liyafar murnar ranar 1 ga watan Oktoba, tun bayan shiga sabon karni.

A cikin jawabin, shugaba Xi ya yi bayani kan buri, da hanya, gami da ka'idoji da aka tsara na raya harkokin kasar Sin. Yanzu shekaru shida ke nan da wucewar hakan, za kuma mu yi waiwaye adon tafiya, mu ga yadda kasar Sin take samun ci gaba a 'yan shekarun nan.

"Kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, ba kawai wani babban al'amari ne na ci gaban al'ummun kasar ba, har ma wani babban abu a tarihin ci gaban dan Adam a duniya. Yau muna iya alfahari da cewa, kasar Sin dake nahiyar Asiya, tana cike da kuzari da damammaki."

Kamar abun da shugaba Xi ya jaddada a jawabin na sa cewa, ci gaba da raya kasar Sin yana dogara kan jama'a, kuma kamata ya yi a yiwa jama'a aiki, kuma gwamnatin kasar Sin tana maida muradun jama'a a gaba da komai.

A yayin ake kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19 a bana, gwamnatin kasar Sin tana bakin kokarinta wajen tattara kwararrun ma'aikatan jinya, da ingantattun na'urorin aikin jinya domin ceton al'umma, kuma dukkan kudaden da aka kashe gwamnati ce ta biya. Hakan ya shaida cewa, jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin, tana maida muradun jama'a a gaban komai.

A nasa bangaren, shehun malami Dai Yanjun, na kwalejin koyon ilimin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana cewa:

"Xi ya sha nanata cewa, ya kamata mu maida harkokin al'umma da muradunsu a gaba da komai, wato samar musu da alfanu shi ne tushen dukkan ayyukan da muke yi. Nasarar da muka samu wajen ganin bayan annobar COVID-19, ta zama tamkar wani yaki ne da jama'a suka yi a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin."

Har wa yau, a jawabin da shugaba Xi ya gabatar, ya nuna cewa, ya kamata kasarsa ta bi tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar, da kara neman bunkasuwa mai dorewa, da kuma zurfafa yin gyare-gyare a gida.

Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, kasarsa za ta ci gaba da bin tafarkin neman bunkasuwa cikin lumana a nan gaba. A yayin da ake yawan samun sauye-sauye a duniya, shirin da kasar Sin ta fitar, wato raya al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, ya riga ya shiga zukatan jama'a. A nasa bangaren, shehun malami Hong Xianghua na kwalejin koyon ilimin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya nuna cewa:

"Kasashe daban-daban na fuskantar matsalolin da suka shafi cututtuka, da bala'u, da yunwa, da ayyukan ta'addanci, da sauyin yanayi, kamata ya yi kasa da kasa su zama tsintsiya madaurinki daya domin daidaita wadannan matsaloli. Kasar Sin tana iya kokarinta wajen neman ci gaba cikin lumana, da himmatuwa wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, wanda hakan zai sa ta kara samun makoma mai haske, kuma duniya ita ma haka."(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China