2020-10-06 16:58:36 cri |
To sai dai kuma daya daga likitocin da suka kula da shugaban lokacin yana asibiti, ya ce babu tabbas game da ko Mr. Trump ya warke gaba daya ko a'a.
Jim kadan kafin barinsa asibiti, Trump ya wallafa sako a shafin sa na twitter, inda a cikin sa yake bayyana aniyar sa ta komawa yakin neman zabe nan ba da jimawa ba. Shugaban mai ci na neman Amurkawa su sake zaben sa ne a zango na biyu, yayin da abokin hamayyar sa na jam'iyyar Democratic, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Joe Biden, ke fatan karbe iko daga Trump a zaben dake tafe cikin wata mai zuwa.
Shi ma dai likitan fadar gwamnatin Amurka Sean Conley, ya shaidawa manema labarai cewa, shugaba Trump na ci gaba da murmurewa cikin sa'o'i 24 da suka gabata, ya kuma cika dukkanin sharuddan barin asibiti, ko da yake ya ce babu tabbas game da warkewarsa kwata kwata.
Shugaba Trump ya koma fadar gwamnati, sa'o'i bayan da sakatariyarsa ta watsa labarai Kayleigh McEnany ta bayyana harbuwa da cutar ta COVID-19. Rahotanni sun tabbatar da cewa, akwai jami'ai da dama dake aiki a fadar White House da suka taba mu'amala da shugaba Trump, wadanda su ma aka tabbatar sun harbu da wannan cuta.(Saminu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China