Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kai wani sabon mataki a fannin samar da hatsi
2020-10-05 17:21:37        cri

Wani rahoto da ma'aikatar kula da ayyukan gona da yankunan karkara ta kasar Sin ta fitar a baya-bayan nan, ya nuna cewa yawan hatsin da kasar take samarwa a duk shekarar zai tsaya kan kg biliyan 650, cikin shekaru 6 a jere.

Aikin samar da hatsi a kasar Sin ya samu ingantuwa sosai tun bayan shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 13. Yawan hatsin da kowanne dan kasa ke samu ya zarce kg 470, wanda ya haura matsakaicin matakin na duniya, haka kuma, ya dara matakin aminci da aka shata a duniya da ya tsaya kan kg 400.

An samu ingantuwar karfin samar da hatsin ne bisa gaggauta aiwatar da dabarar kiyaye gonakin samar da hatsi da kuma ta amfani da fasahar zamani. Kasar Sin na aiwatar da tsarin kare kasar noma mai tsanani, sannan tana kiyaye sharadin da aka gindaya na noma kan fili mai fadain kadada miliyan 120 da kuma aiwatar da tsarin musamman na kare kasar noma ta dindin din. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China