![]() |
|
2020-10-05 17:19:45 cri |
A cewar Danjuma Elisha, shugaban hukumar tsaron fararen hula wato Civil Defence, an kama mutanen ne bisa umarnin da gwamnan jihar, Hope Uzodinmma ya bayar na farwa masu hakar ma'adinai ta haramtacciyar hanya a jihar.
A cewar shugaban hukumar tsaron, hakar ma'adinai ta haramtacciyar hanya na mummunan tasiri kan rayuwar al'ummar jihar, yana mai cewa daya ce daga cikin abubuwan dake sabbaba zaizayar kasa da ambaliya.
Ya ce an yi nasarar kama mutanen ne biyo bayan hadin gwiwar da aka yi tsakanin jami'an tsaro a jihar.
A baya-bayan nan ne gwamnatin jihar, ta sanar da haramta hakar ma'adinai ta haramtacciyar hanya tare da ba hukumomin tsaro umarnin cafke wadanda ake zargi da gudanar da aikin. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China