Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakatare Janar na MDD ya yi kira da a tsagaita bude wuta a duniya yayin tunawa da ranar yaki da rikici ta duniya
2020-10-03 16:54:34        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya jaddada kira da a tsagaita bude wuta a duniya, yayin da ake tunawa da ranar yaki da rikici ta duniya a jiya Juma'a, wanda ya gudana bana a lokacin da ake fuskantar mummunan tasirin annobar COVID-19 a kan harkokin tattalin arziki da zaman takewa.

A sakonsa domin ranar, Antonio Guterres ya tunatar da jama'ar duniya cewa, hakkin da ya rataya a wuyansu a wannan rana shi ne, dakatar da fadace-fadace, tare da mayar da hankali ga yakar COVID -19 da ta kasance makiyar dukkan bil adama.

A cewarsa, tsagaita bude wuta zai saukaka wahalhalu da rage barazanar yunwa da bude kofa ga sulhu don samun zaman lafiya.

Ya ce loakci ya yi da ya kamata a matse kaimi, a samu kwarin gwiwa daga tunanin Gandhi da kuma ka'idojin MDD.

A shekarar 2007 ne babban zauren MDD ya ayyana ranar 2 ga watan Oktoba a matsayin ranar yaki da rikici ta duniya, wanda ya zo daidai da ranar haihuwar Mahatma Gandhi, da ya jagoranci fafutukar neman 'yancin kan Indiya, ya kuma asassa falsafar yaki da rikici. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China