Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Farfadowar tattalin arzikin kasar Sin zai karfafa imanin kasuwannin duniya
2020-09-30 22:20:41        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaidawa taron manema labarai Larabar nan cewa, bankin duniya ya fitar da wani rahoto dake kara hasashen da ya yi game da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, abin da ke nuna cewa, al'ummar duniya sun yi na'am da gaggarumin ci gaban da kasar Sin ta cimma, wajen kara daukar matakan kandagarki da hana yaduwar annobar COVID-19 gami da raya tattalin arziki da inganta rayuwar jama'a.

A don haka, farfadowar tattalin arzikin kasar Sin, na da matukar muhimmanci wajen kara imanin kasuwannin duniya.

A ranar 28 ga wata ne, bankin duniya ya fitar da wani rahoto kan ci gaban tattalin arzkin yankin gabashin Asiya da fasifik, inda ya kara hasashen da ya yi kan bunkasar tattalin arzikin kasar Sin zuwa kaso 2 cikin 100 a wannan shekara, karuwar kaso 1 kan hasashen da ya yi a watan Yuni. Haka kuma bankin na duniya ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar ta Sin, zai bunkasa da kaso 7.9 cikin 100 a shekara mai zuwa, inda ya dogara kan wasu manyan dalilai, kamar samun alluran riga kafin COVID-19, da dorewar farfadowar tattalin arziki. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China