Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Kasar Amurka ce ke kan gaba wajen yi wa kasar Sin kutse ta Intanet
2020-09-29 21:37:37        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin, ya bayyana Talatar nan yayin taron manema labarai cewa, har yanzu kasar Sin ce ke daya daga cikin kasashen da suka fi fama da matsalar kutse ta Intanet, kuma matsalar ma ta fi kamari a lokacin yaki da annobar COVID-19. Kuma Amurka ce ke kan gaba wajen yiwa kasar Sin Kutse ta Intanet.

Wang Wenbin ya jaddada cewa, kutse ta Intanet, babban kalubale ne da dukkan kasashe ke fama da ita. A don haka,a koda yaushe kasar Sin take kira ga kasashen duniya, da su karfafa tattaunawa da hadin gwiwa bisa tsarin mutunta juna, da nuna daidaito da fahimtar juna, a kuma magance wannan kalubale tare.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China