Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin yanayin tsakiyar Kaka na al'ummar Sinawa
2020-09-30 09:08:18        cri

Bikin Zhongqiu ko bikin yanayin tsakiyar kaka, yana daga cikin muhimman bukukuwan gargajiya na al'ummar Sinawa, wanda a kan yi shi a ranar 15 ga watan 8 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, bikin na wannan shekara ya fado ne a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 2020. Zhongqiu yana nufin yanayi na tsakiyar Kaka.

A wannan rana, farin wata ya kan cika da'irarsa, yana kuma yin haske sosai, a lokacin ne kuma al'ummar Sinawa kan hango duniyar wata, suke kuma kewar iyalansu. Shi ya sa Sinawa ke daukar bikin a matsayin bikin haduwar iyali. A don haka, a yayin wannan biki, Sinawa a duk inda suke a duniya, idan suna da dama, su kan koma gida don haduwa da iyalansu.

Bikin ya samo asali ne daga Ibada, inda sarakunan gargajiya na wancan zamani, suke gudanarwa inda suke bautawa duniyar Rana a lokacin Bazara, kana a lokacin Kaka su kan bautawa duniyar Wata. Amma daga bisani, wannan al'ada ta zama ruwan dare a tsakanin al'umma, ana sannu a hankali, ta zama wani biki da jama'a su kan yi.

Haka kuma, bincike ya nuna cewa, baya ga yadda bikin ya samu karbuwa a cikn al'ummar Sinawa, akwai wasu sassan kudu maso gabashin Asiya da ake gudanar da wannan biki, duk da cewa, bikin ya kan sha bamban daga wata kasa zuwa wata, ko daga wannan yanki zuwa wannan yanki. Amma dai, tushen bikin, shi ne biki ne na Sinawa.

Akwai wasu tatsuniyoyi da suka shahara game da wannan biki, ko suke da alaka da bikin. Ban da kallon wata, akwai kuma cin Wainar wata- mai kama da siffar wata da kuma haduwar iyali.

Baya ga haduwar iyali, ana kuma nuna godiya ga amfanin gonan da aka samu, wato lokacin girbin amfanin gona.

Baki daya dai bikin, yana nuna muhimmancin haduwar iyali, kamar lokutan sallah da bikin Kirsimeti da sauran bukukuwn gargajiya a kasar Hausa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China