Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cin zarafin kamfanonin kasar Sin da 'yan siyasar Amurka suka yi ba zai samu goyon-bayan jama'a ba
2020-09-28 22:08:56        cri

Wani alkalin babbar kotun tarayyar Amurka, wato mai shari'a Carl Nichols na kotun tarayyar dake gundumar Columbia, ya dakatar da umarnin da shugaba Dornald Trump ya gabatar, game da haramtawa kamfanin nan dake yada kananan faya fayan bidiyo na TikTok na kasar Sin gudanar da ayyukansa a Amurka. Kotun dai ta dakatar da umarnin shugaban na Amurka ne a jiya Lahadi, sa'o'i 4 gabanin cikar wa'adin fara aiki da umarnin. Duk da cewa kura ta dan lafa, amma har yanzu kamfanin TikTok yana cikin halin ja-in-ja da bangaren Amurka.

Yayin da wata babbar kotun tarayyar Amurka ta dakatar da umarnin shugaban kasar Amurka game da haramta amfani da manhajar WeChat ta kasar Sin, sai ga shi wata kotun tarayya ta daban ta sake dakatar da yunkurin wasu 'yan siyasar Amurka na cin zarafin kamfanonin kimiyya da fasahar kasar Sin. Wannan ya sake shaida cewa, irin cin zalin kamfanonin kasar Sin da gwamnatin Amurka ta yi ba shi da tushe bisa doka balle makama, kana, yin babakere da nuna fin karfi da Amurka ta yi yana gamuwa da fushin al'umma sosai.

Manazarta sun yi nuni da cewa, gwamnatin Amurka ta yi ikirarin cewa wai TikTok tana amfani da bayanan masu mu'amala da manhajar ta hanyar da ba ta dace ba, amma ko hukumar leken asirin Amurka CIA ma ta ce babu shaidu kan wannan ikirari. Tun da babu shaidu, sai kuma aka fake wajen dorawa TikTok laifin kawo barazana ga tsaron Amurka, da cin zarafinsa, har ma da tilasta masa sayar da ayyukansa a Amurka…

Gaskiyar magana ita ce, yarjejeniyar da manhajar TikTok ta kulla da kamfanonin Amurka ba ciniki ne zalla ba, cin zarafi ne na siyasa, kana babbar karya ce da wasu 'yan siyasar Amurka suka kitsa domin neman cimma muradun siyasa. Duk da cewa wannan hukuncin kotun ya sa TikTok zai samu lokaci kadan na hutawa, amma har yanzu yana takun saka da bangaren Amurka.

Ya kamata Amurka ta sani, a matsayinta na kasar da take haye wahalhalu da dama sa'annan take ci gaba a koda yaushe, kome rintsi Sin ba za ta mika wuya ga duk wata barazanar da ake mata ba, kana babu shakka za ta yi duk kokarin da ya dace na kare hakkokin kamfanoninta.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China