Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Najeriya suna murnar ranar 1 ga watan Oktoba tare
2020-10-01 15:22:20        cri


Yau 1 ga wata, rana ce muhimmiya ga kasar Sin da tarayyar Najeriya, wato an cika shekaru 71 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, Najeriya ita ma ta cika shekaru 60 cif da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da wasu 'yan Najeriya a kasar Sin da kuma wani dan kasar Sin dake aiki a Najeriya, domin jin ta bakinsu irin ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ambasada Bakori Aliyu Usman, wani gogaggen jami'in diflomasiyyar Najeriya ne wanda ya yi shekaru 10 gaba daya yana aikin jakadanci a kasar Sin. A yayin da kasashen biyu ke murnar ranar 1 ga watan Oktoba a lokaci guda, Ambasada Bakori ya yi karin haske kan nasarorin da aka samu wajen inganta mu'amala tsakanin kasashen biyu.

Bana duk duniya na fuskantar barazanar yaduwar cutar mashako ta COVID-19. Ambasada Bakorin ya tabo magana kan ta yaya annobar ta shafi huldar Sin da Najeriya, ya kuma taya kasashen biyu murnar ranar 1 ga watan Oktoba.

Kamar abun da Ambasada Bakori Aliyu Usman ya fada, dangantakar Sin da Najeriya tana bunkasa cikin sauri a wadannan shekarun da suka gabata, musamman a fannonin da suka shafi kasuwanci, da tattalin arziki, da al'adu, da ayyukan noma da kuma fannin ilmi. A halin yanzu akwai daliban Najeriya da dama wadanda suke karatu a jami'o'in kasar Sin, Bello Nasiru Abdullahi na daya daga cikinsu.

Bello Nasiru Abdullahi, dalibi dan jihar Kano ne wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a fannin kimiyyar tattalin arzikin gona a jami'ar koyon ilimin aikin gona ta lardin Gansu na kasar Sin. Ya ce, duk da cewa bai dade da fara karatu da zaman rayuwa a kasar Sin ba, amma yadda mutanen Sin suke karbar baki da nuna musu karamci ya burge shi kwarai da gaske.

Bello Nasiru Abdullahi ya kuma taya kasashen biyu murnar zagayowar wannan rana, da yin kira ga mutanen kasashen biyu.

Har wa yau, a halin yanzu akwai mutanen kasar Sin da dama wadanda suke aiki da zama a sassa daban-daban na Najeriya, wadanda suke bayar da gudummawa sosai ga inganta zumunci da mu'amala tsakanin kasashen biyu. Peter Huang, wani ma'aikacin kamfanin gine-ginen kasar Sin ne, wanda ya yi shekaru kusan hudu yana aiki a Najeriya. Ya ce, wata rana ko ya bar aiki a Najeriya, ba zai manta da irin taimako da mutanen kasar suka ba shi ba. Ya bayyana cewa:

"Na dade ina aiki a Najeriya, musamman tun barkewar cutar COVID-19 a bana, ban tafi ko'ina ba sai babban birnin Abuja. Saboda na gaza wajen komawa kasa ta Sin, ina karancin abubuwan kasata sosai, kuma ba wanda zai taho min da su. Amma kwanan baya, wani abokina dan Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatu a kasar Sin, ya kira ni ya ce zai dawo Najeriya, zai kuma iya dauko min abubuwan da nake bukata daga kasar Sin. Gaskiya ya burge ni sosai, ban taba tunanin shi zai iya taho min da abubuwa daga kasar Sin ba, saboda shi kansa zai sayo wa matarsa da yaransa abubuwa da dama. Gaskiya na ji dadi matuka."

Peter Huang ya ce, ya tambayi wannan aboki nasa ko menene dalilin da ya sa yake son taimaka masa, sai ya ce:

"Ya amsa min cewa, ina son taimakawa mutanen kasar Sin saboda suna taimaka mana wajen inganta muhimman ababen more rayuwar jama'a da dama, suna taimakawa ci gaban kasarmu. Kuma yana da yakinin cewa, in mutanen Najeriya suka je kasar Sin, mutanen kasar su ma za su taimake su. Wannan maganarsa ta burge ni sosai. Taimakekeniya tsakaninmu za ta kara dankon zumunta da samun fahimtar juna tsakaninmu a cikin dogon lokaci."

Peter Huang ya ce yana farin-ciki sosai da ganin ranar samun 'yancin kai ta Najeriya da ranar kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin ta zamanto a rana guda, inda ya ce:

"Wannan rana ce ta farin-ciki kwarai da gaske, muna fatan Allah zai karfafa zumunci tsakanin Sin da Najeriya, muna kuma fatan al'ummun kasashen biyu za su kara jin dadin wannan rana." (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China